Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa na naira triliyan 8 da biliyan dubu 83 wanda yace za’ayi amfani da shi wajen samar da cigaba, yaki da talauci da gina kayan more rayuwa.

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari REUTERS/Stringer
Talla

Kasafin kudin ya gaza na bara wanda ya kai naira triliyan 9 da biliyan dubu 120.

Buhari yace suna saran samun kudaden shigar da suka kai sama da naira triliyan 6 a shekara mai zuwa, yayin da zasu kashe naira sama da triliyan 3 wajen gudanar da manyan ayyuka da kuma sama da naira triliyan 2 wajen biyan bashi.

Domin tabbatar da zaman lafiya a Naija Delta, an ware naira biliyan 65 domin cigaba da shirin amnesty a cikin kasafin shekara mai zuwa. Har ila yau an ware naira biliyan 45 domin sake gina yankin arewa maso gabas, yayin da aka ware naira biliyan 10 domin fara aikin hukumar sake gina yankin arewa maso gabas.

Domin sake tallafawa masu kananan da matsakaitan masana’antu, wanda shine shirin mu na gina masana’antu mun ware naira biliyan 15 domin karfafa bankin noma da kuma rancen naira biliyan 10 domin saukakawa masu kanana na matsakaitan masana’antu wajen karbar rance

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.