Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Buhari ya sake jagorantar taron kasashen Yankin Tafkin Chadi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake jagorantar wani taron shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi inda suka sake tattaunawa, kan kalubale na matsalolin tsaro dake ci musu tuwo a kwarya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Shugaba Buhari ya ce taron, ci gaba ne kan makamacinsa da suka yi a karshen watan Nuwamba a birnin N’djemena, kamar yadda rahoton kwamitin da suka kafa na tsara hanyoyin tabbatar da kawo karshen Boko Haram ya bukata.

Taron na ranar Asabar,ya mayarda hankali kan sabbin hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a sassan kasashen na Yankin Tafkin Chadi da kuma yadda za’a tunkari sabon kalubalen yadda kungiyar ta Boko Haram ke samun taimako daga kungiyoyi makamantanta na kasashen ketare.

Taron ya samu halartar shugaban Chadi Idris Deby, shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issufou da kuma Fira Ministan Kamaru Philmon Yang, wanda ya wakilci shugaban kasar Paul Biya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.