Isa ga babban shafi
Chadi

Faransa ta dafawa Chadi da kudi milyan 50 na Euros

Kasar Faransa ta sanar da ware milyan 40 na Euros a matsayin bashi ga kasar Chadi, kudadden da za su taimaka domin biyan albashin ma’aikata da tsofin ma’aikata da suka yi ritaya a kasar.

Idriss Déby Shugaban kasar Chadi
Idriss Déby Shugaban kasar Chadi Ludovic MARIN / AFP
Talla

Yarjejeniya da kasashen biyu suka cimma na nuni cewa gwamnatin Chadi za ta yi amfani da milyan 30 wajen biyan albashin watan Disemba zuwa ga wasu ma’aikata dubu 90 fararren hula yayinda sauaran milyan 10 zasu taimaka domin biyan wasu albashi da ake bin Gwamnatin na watanni uku.

Faransa ta yi alkawalin dafawa Chadi da milyan 50 a lokacin da aka gudanar da wani taron masu hannu da shiuni na Paris a watan Satumba na shekara ta 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.