Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Buhari zai ziyarci Maiduguri

Yau Laraba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ziyarci Maiduguri, kwanaki bayan kazamin harin da mayakan kungiyar boko Haram suka kai, wanda yayi sanadiyar rasa dimbin rayukan sojin Najeriya.

Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke hutun da ya shirya tafiya a karshen wannan mako domin cigaba da tattauna dabarun kawo karshen wannan rikici dake cigaba da hallaka jama’a a Borno.

A cikin wannan mako ne mayakan Boko Haram suka hallaka wasu manoma hudu a dai dai lokacin da suke tsaka da aikinsu gab da garin Ali Goshen da ke wajen birnin Maidugurin jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu da suka tsira da rayukansu a harin na boko Haram, sun ce mayakan sun zo garin ne saman baburan su fiye da 30 inda suka zabi mutane 4 da suka harbe suka bar sauran.

Baba Isa Bukar wani mazaunin Maiduguri ya bayyana fatar da suke da shi dangane da ziyarar Shugaban Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.