Isa ga babban shafi
Duniya

Akwai barazanar hana jama’a gudanar da addinin su

Wata Kungiyar mabiya darikar Katolika a Duniya ta ce akwai barazanar hana jama’a gudanar da addinin su daga kasa guda dake cikin ko wadanne kasashe 5 a fadin duniya.Rahotan binciken kungiyar yace ya gano kasashe 21 da matsalar tafi kamari bayan kwashe shekaru biyu tana gudanar da bincike.

Wasu musulmai dake tattaunawa a harabar masallaci a China
Wasu musulmai dake tattaunawa a harabar masallaci a China GOH CHAI HIN / AFP
Talla

Wannan kungiya ta bayyana kasashen da wannan matsala tafi kamari da suka hada da Jamhuriyar Nijar da Najeriya da Myanmar da India da kuma China.

Rahotan kungiyar yace ya samu korafe korafe na cin zarafin mabiya wasu addinai a kasashe 17 da suka hada da Algeria da Turkiya da kuma Rasha.

Wannan dai shine karo na 14 da kungiyar ke gabatar da rahotan binciken da take gudanarwa wanda ya shafi kasashe 196 na duniya, da ake gudanar da shi ko wane shekaru 2 tare da taimakon yan Jaridu masu zaman kan su.

Shugaban reshen kungiyar dake Faransa, Marc Fromager yace sun gano hare haren da ake kaiwa yancin gudanar da addini, yayin da matsalar tafi kamari a China da India.

Fromager yace a China ana lalata mujami’u da kuma hana yan kabilar Uighur Musulmi yin azumin watan Ramadana, yayin da ake azabtar da mabiya addinin Budha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.