Isa ga babban shafi
Najeriya - INEC

Jam'iyyu 56 ne cikin 91 za su tsaya zabe a Najeriya - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce Jam’iyyun siyasa 56 ne cikin 91 da ta yi wa Rijista suka shirya tsayawa takarkaru daban-daban yayin babban zaben kasar da ke karatowa cikin shekara mai kamawa ta 2019.

INEC ta bai wa al’ummar Najeriyar tabbacin cewa dukkanin kayan aiki za su isa ko’ina akan lokaci yayin zabukan na shekarar 2019.
INEC ta bai wa al’ummar Najeriyar tabbacin cewa dukkanin kayan aiki za su isa ko’ina akan lokaci yayin zabukan na shekarar 2019. Ventures Africa
Talla

A cewar hukumar ta INEC ta so ace ilahirin jam’iyyun kasar 91 da suka yi rijista da ita ne za su samu damar shiga zaben na 2019 amma babu yadda za ta yi la’akari da cewa dole sai jam’iyyun sun samu rijistar zaben na 2019, wanda kuma akalla jam’iyyu 35 suka gaza yi.

Hukumar zaben Najeriyar INEC ta kuma kara jaddada kudurin na gudanar da sahihin zabe ba tare da magudi ba, yayin ilahirin zabukan da za su gudana a sassan kasar cikin 2019.

Ka zalika INEC ta bai wa al’ummar Najeriyar tabbacin cewa dukkanin kayan aiki za su isa ko’ina akan lokaci, domin kuwa tana da shiryayyen tsari a kasa da baza a samu jinkiein fara zabe ba a ranakun da ta tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.