Isa ga babban shafi
Najeriya

Bukola Saraki zai tsaya takarar neman Shugabancin Najeriya a 2019

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya bayyana aniyar sa na tsayawa takarar zaben shekara mai zuwa a Jam’iyyar PDP domin kalubalantar shugaba Muhammadu Buhari.

Bukola Saraki Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya
Bukola Saraki Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin gabatar da takarar sa wajen taron matasa a Abuja, Saraki yace ya zama dole su bada gudumawa wajen magance matsalolin da suka addabi kasar.

A baya Bukola Saraki ya bayyana cewa zai yi nazari domin shigar da takarar sa a lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta ‘Bloomberg’ mai hedikwata a birnin New York, inda ya ce yana da kwarin gwiwar zai iya kawo kyakkyawan sauyi a al’amuran Najeriya.

Saraki ya kara da cewa, ba zai yi mamaki ba, idan har gwamnatin shugaba Buhari ta yi amfani da jami’an tsaro a zaben 2019, ganin cewa ‘yan Najeriya sun yanke kyakkyawan fatan da suke yiwa gwamnatin mai ci.

Shugaban majalisar dattijan ya ce a ra’ayinsa kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta maido da tallafin sauke farashin man fetur, ta hanyar ware wa tallafin kasafi na musamman, domin baiwa bangaren ‘yan kasuwa damar shiga sha’anin shigo da man fetur daga kasashen ketare.

A cewar Saraki, Najeriya tana bukatar jagorancin shugaban kasa mai ra’ayin ciyar da fannin cinikayya gaba kuma wanda zai iya daukar matakan nan take wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke damun sassan kasar.

Mohammed Isa, Sakataren yada labaran sa, yayi mana tsokaci akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.