Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An dage rantsar da Mnangagwa bayan shigar da karar Jam'iyyar MDC

Ma'aikatar shari'ar Zimbabwe ta yi umarnin dakatar da shirin rantsar da shugaban kasar mai jiran gado Emmerson Mnangagwa bayan da babbar Jam'iyyar adawa ta MDC ta gabatar da kara a gaban kotu inda ta ke kalubalantar sakamakon zaben da aka yi wanda ya nuna cewa shugaban ke da nasara.

Jam'iyyun adawar a Zimbabwe na kalubalantar nasarar Emmerson Mnangagwa wanda ke matsayin mataimakin shugaban Robert Mugabe tsawon shekaru kafin murabus dinsa a bara.
Jam'iyyun adawar a Zimbabwe na kalubalantar nasarar Emmerson Mnangagwa wanda ke matsayin mataimakin shugaban Robert Mugabe tsawon shekaru kafin murabus dinsa a bara. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Ministan Shari'ar kasar Ziyambi Ziyambi ya ce za a dage rantsar da shugaban ne sakamakon kalubalantar zaben da babbar Jam'iyyar adawa ta MDC ta yi har zuwa lokacin da za a fara sauraron shari'ar.

Jameson Timba, tsohon dan Majalisar MDC, ya bayyana cewar su na kotu domin gabatar da takardun su.

Zaben na Zimbabwe ya haifar da tashin hankali saboda zargin magudi, abinda ya sa sojoji suka yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen harbe mutane 6 har lahira yayin wata zanga-zangar adawa da zargin tafka magudi a zaben gabanin sanar da sakamako.

Kafin yanzu dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya bukaci samun gamsuwa daga ilahirin jam'iyyun adawar kasar kafin amincewa da sakamakonsa.

Zaben dai shi ne irinsa na farko da aka taba gudanarwa a Zimbabwe bayan fiye da shekaru 30 da Robert Mugabe ya shafe a karagar mulki kuma karkashin Jam'iyya guda kafin murabus dinsa a bara.

Emmerson Mnangagwa wanda ya karbi ragamar shugabancin kasar bayan Murabus din Robert Mugabe, ya kuma tsaya takara a zaben, Mugabe da kansa ya bukaci al'ummar kasar kan kada su zabe shi amma kuma ya yi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.