Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan bindiga sun balle gidan yari a yankin Inglishi na kasar Kamaru

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa fursunoni 160 ne suka tsere daga wani gidan yari da ke yankin Arewa maso yammacin kasar.Bayanai sun ce ‘yan bindiga kusan 50 ne suka afka wa gidan yarin tare bude wuta akan jami’an tsaro, inda daga bisani su ka balle kofofin gidan yarin.

Gidan yarin da yan bidiga suka balle a yankin turancin Iglishi na kasar Kamaru 29-07-208
Gidan yarin da yan bidiga suka balle a yankin turancin Iglishi na kasar Kamaru 29-07-208 fricanews.com
Talla

Wani jami’in gwamnatin lardin da lamarin ya faru William Emvouto Bbita, ya ce bayan balle kofofin gidan yarin, maharan sun banka wa baki dayan gidan yarin wuta.

A cewar Mista William, maharan sun zo ne a cikin shiri sosai, domin kuwa wasu daga cikinsu na dauke da jarkuna cike da man fetur wanda suka yi amfani da shi wajen banka wa ginin wuta.

Tuni dai mahukuntan gidan yarin suka roki fursunonin da suka gudu domin tsira da rayukansu da su gabatar da kansu ga jami’an tsaro, kuma a cewar wata majiya a gidan yarin, za a tattara su don cigaba da tsare su a gidan kurkukun garin Bamenda.

Yankunan da ke amfani da turancin Ingilishi na kasar ta Kamaru na fama da tashe-tashen hankula, kuma a cewar MDD lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da tilasta wa wasu akalla dubu 180 barin gidajensu a cikin shekaru biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.