Isa ga babban shafi
Kamaru

Gwamnatin Kamaru ta tsayar da ranar zaben shugaban kasa

Shugaban Kamaru Paul Biya, ya sanya hannu kan wata dokar amincewa da shirin gudanar da zaben shugaban kasar da za’ayi ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa.

Paul Biya, shugaban kasar Kamaru.
Paul Biya, shugaban kasar Kamaru. AFP Photo/Lintao Zhang
Talla

Wannan ya kawo karshen cece kucen da kae cewar wata zaben ba zai yiwu ba a cikin wannan shekara.

Shugaba Paul Biya wanda yak e jagorancin kasar Kamaru tun daga shekarar 1982 bai bayyana shirin san a shiga zaben shugaban kasar ba duk da kiraye kirayen da magoya bayan sa keyi na ganin ya gabatar da takarar sa.

Tuni Jam’iyyar adawa ta SDF ta gabatar da shugaban ta Joshua Osih a matsayin dan takaran zaben domin fafatawa da shugaba Biya idan ya yanke hukuncin tsayawa takara.

Sauran masu sha’awar tsayawa takarar zaben sun hada da Akere Muna, lauya kuma tsohon mataimakin shugaban kungiyar Transparency International da Maurice Kamto, shugaban Jam’iyyar MRC.

Zaben na zuwa ne a wani lokaci da kasar ke fuskantar tahse tashe hankula daga Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi inda wasu daga cikin mutanen yankin ke fafutukar ganin sun balle sun kuma kafa kasar Ambazonia.

Tuni Jam’iyyar adawa ta SDF ta gabatar da shugaban ta Joshua Osih a matsayin dan takaran zaben domin fafatawa da shugaba Biya idan ya yanke hukuncin tsayawa takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.