IIPOB ta bukaci Igbo su zauna gida don tunawa da ranar Biafra
Kungiyar IPOB da ke fafutukar kare maradun ‘yan kabilar Igbo tare da ballewar Biafra daga Najeriya, ta bukaci mazauna yankin da su zauna gidajensu a wannan laraba, domin tunawa da ranar shelanta ballewar yankin da kuma abubuwan da suka faru sakamakon yakin basasar kasar tsakanin 1967-1970.
Wallafawa ranar:
A shekarar da ta gabata gwamnatin Najeriya ta ayyana kungiyar ta IPOB a matsayin ta ta’addanci sakamakon yadda take tayar da hankula da kuma karya dokokin kasar, sannan aka hana magoya bayanta gudanar da taruruka ko kuma gangami a duk fadin kasar.
Gwamnatin jihar Anambara daya daga cikin jihohi 5 da ke yankin na Kudu maso gabashin Najeriya, ta yi gargadin cewa za ta ladaftar da duk ma’aikacin da ya kaurace wa aikinsa a yau.
A jihar Ebonyi kuwa, gwamnati ta ce duk dan kasuwar da ya karba wannan kira na kasancewa gida a wannan laraba, za ta karbe shagonsa, yayin da a sauran jihohi irinsu Abia, rundunar ‘yan sanda ta bai wa wadanda ke bukatar ci gaba da harkokinsu na kasuwanci tabbacin samun kariya daga jami’anta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu