Isa ga babban shafi
Mali

Fulani na bukatar kariya daga gwamnatin kasar Mali

Dubun dubatar Fulani ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali, domin nuna bacin ransu dangane da yadda ake kai wa kabilar hare-hare bisa zargin cewa ‘yan ta’adda ne.

Kabilar Fulani na zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali karkashin inuwar kungiyarsu mai suna Tabital Pulaaku-Mali
Kabilar Fulani na zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali karkashin inuwar kungiyarsu mai suna Tabital Pulaaku-Mali © ANNIE ROSEMBERG / AFP
Talla

Fulani, sun fara fuskantar matsala a kasar ta Mali ne sakamakon bayyanar wata kungiya ta ‘yan ta’adda a garin Macina, garin da ke matsayin babbar cibiya ga kabilar ta Fulani a kasar.

Kungiyar ‘’Andal Pulaako Mali’’ wadda ta bukaci a gudanar da zanga-zangar a jiya alhamis, ta yi zargin cewa an kashe Fulani akalla 25, raunata wasu da kuma kona gidajensu duk da cewa ba su da alaka da wata kungiya ta ta’addanci.

To sai dai yayin da wasu ke zargin su da ta’addanci, su ma kansu ‘yan kabilar ta Fulani ba su tsira daga hare-haren da kungiyoyin ta’addanci ke kai wa a sassa daban daban na kasar ta Mali ba, lamarin da ya sa kungiyar ta Andal Pulaako Mali ta bukaci mahukuntan kasar da su bai wa Fulanin kariya ta tsaro.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.