Isa ga babban shafi
Habasha

Firaministan Habasha ya yi murabus

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn ya yi marabus daga mukaminsa bayan wani dadadden rikicin siyasa, matakin da ake kallo a matsayin sabon abu a kasar da ke yankin gabashin Afrika.

Firaministan Habasha mai murabus Hailemariam Desalegn
Firaministan Habasha mai murabus Hailemariam Desalegn Photo: Reuters/Tiksa Negeri
Talla

Firaminista Hailemariam Desalegn da ya dare kan kujersa tun shekarar 2012, ya yanke shawarar murabus ne bayan watannin da aka dauka ana fama da jerin zanga-zangar adawa da gwamnati da kuma alamomin da suka bayyana na baraka a hadakar jam’iyya mai mulki.

A jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin, Hailemariam ya ce, ya yi aiki tukuru don magance matsalolin da Habasha ke fama da su, kuma a cewarsa, ya yi amanna, matakin da ya dauka na murabus na cikin magance matsalolin.

Firaministan ya ce, gwamnatinsa karkashin jam’iyyar hadaka ta EPRDF za ta sake kafa sabon tarihi ta hanyar mika mulki cikin lumana a kasar.

Sai dai Hailemariam zai ci gaba da jagoranci har zuwa lokacin da Majalisar Dokokin kasar da kuma jam’iyyar za su tabbatar da murabus dinsa a hukumance.

Titunan birinin Addis Ababa sun yi tsit bayan sanarwar ba za ta ta murabus din Firaministan.

Duk da cewa, Habasha na daya daga cikin matalautan kasashe a Afrika, Hailemariam ya ci gaba da kokarin inganta tattalin arzikin kasar.

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da wanda zai maye gurbinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.