Isa ga babban shafi
Najeriya

WHO ta koka kan yaduwar cutar Lassa a Najeriya

Hukumar kula da Lafiya ta Duniya WHO, ta ce akalla mutane 450 ne suka kamu da cutar zazzabin Lassa a Najeriya, cikin kasa da makwanni biyar.Tsawon kusan shekaru biyu kenan Najeriya na fama da matsalar bullar cutar ta Lassa wadda bera ke haddasawa a sassan daban-daban na kasar, lamarin da a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka.

Tsawon kusan shekaru biyu kenan Najeriya na fama da matsalar bullar cutar ta Lassa wadda bera ke haddasawa a sassan daban-daban na kasar, lamarin da alokuta da dama kan haddasa asarar rayuka.
Tsawon kusan shekaru biyu kenan Najeriya na fama da matsalar bullar cutar ta Lassa wadda bera ke haddasawa a sassan daban-daban na kasar, lamarin da alokuta da dama kan haddasa asarar rayuka. wikimedia
Talla

Shugaban sashin yaki da cutar Lassa a karkashin hukumar lafiya ta Duniya a Najeriya, Dr Emmanuel Musa, ya ce abin damuwa ne ganin yadda aka samu karuwar wadanda suka kamu da zazzabin a kasar, idan aka kwatanta da shekarar bara.

Tun bayan barkewar cutar a Njeriya cikin shekarar nan, ta fantsamu a jihohin kasar da dama galibi arewaci inda a jihar kano kadai ta hallaka fiye da mutum shida, yayinda ake da karin mutane da dama da ke karbar kulawar gaggawa.

Yanzu haka dai akwai tarin mutane da ke fama da cutar ta Lassa a jihohin Kogi, Taraba Kano da sauran sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.