Isa ga babban shafi
Liberia

An rantsar da Goerge Weah a matsayin shugaban Liberia

Yau ne ake rantsar da zababben shugaban Liberia, George Weah da zai gaji Ellen Johnson Sirleaf da ta shafe shekaru 12 kan karagar mulkin Liberia.

Sabon shugaban Kasar Liberia kuma zakaran kwallon duniya George Weah, tare da tsohuwar shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf gabanin mika mulki yayin bikin rantsar da shi a safiyar yau.
Sabon shugaban Kasar Liberia kuma zakaran kwallon duniya George Weah, tare da tsohuwar shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf gabanin mika mulki yayin bikin rantsar da shi a safiyar yau. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

A karon farko kenan tun shekarar 1944 da wani zababben shugaba ke mika mulki cikin lumana ga wani zababben shugaban a kasar wadda ta yi fama da yakin basasa.

Weah, tsohon gwarzon dan kwallon kafar duniya, ya lashe zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a cikin watan Disamban bara da kashi 61.5 bayan ya doke mataimakin shugaban kasa, Joseph Bokai wanda ya samu kasa da kashi 32.

Sai dai masana siyasa na cewa, akwai tarin kalubale da ke gaban sabon shugaban musamman ta fannin habbaka tattalin arzikin kasar da ke cikin mawuyacin hali.

Tarihin George Weah

George Manneh Weah kamar yadda ake kiransa a Liberia, ya taso ne a yankin Clara, daya daga cikin kazaman unguwanni masu fama da talauci a birnin Monrovia kuma kakarsa mai suna Emma Klonjlaleh, ita ce ta reni shi har zuwa lokacin da ya shahara a shekarar 1990 a fannin kwallon kafa.

Tsohon dan wasan wanda ya taba lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, ya yi kokarin amfani da matsayinsa wajen samun karbuwa a wurin mutanen Liberia.

Shi ne dan wasan Afrika na farko da ya lashe kyautar Ballon d'Or, kuma ya taka leda a manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai da suka hada da PSG da AC Milan da Monaco da Manchester City tsakanin 1989 zuwa 2003, wato lokacin da kasarsa ta Liberia ke fama da yakin basasa.

Weah mai shekaru 51 kuma dan kabilar Kru ya ajiye karatu a lokacin kuruciyarsa amma daga bisani ya samu kwalin digiri bayan ya sha matsin lamba daga ‘yan adawa da ke cewa, ai bai kammala karatu ba, abin da ya sa suke ganin bai shirya zama shugaban kasa ba.

Da dama daga cikin mutanen Liberia musamma matasa na matukar nuna kauna ga Weah saboda rawar da ya taka wajen tallafa musu bayan fama da yakin basasa.

A shekarar 2005 ya fara bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar neman kujerar shugaban kasa, sai dai ya sha kashi a hannun Ellen Johnson Sirleaf, sannan ya sake tsayawa takara a 2011 duk da haka bai kai labari ba.

Tsohon dan wasan na da yara uku kuma a can baya ya taba komawa addinin Islama daga Kirista amma daga bisani ya sake sauya sheka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.