Isa ga babban shafi
Najeriya

El-Rufa'i zai dawo da korarrun malamai bakin aiki

Kungiyar malaman makaranta NUT ta janye yakin aikin sai baba ta gani da ta shiga a jihar Kaduna, kwanaki 10 da suka gabata, don tilastawa gwamnan jihar Malam nasir El Rufa’I janye kudurinsa na korar malaman makarantun jihar kusan dubu 22.Matakin na zuwa bayan da gwamnatin Kadunar ta sanar da bayar da dama ta biyu ga korarrun malaman don su kara nuna fasaharsu.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Naseer El Rufa'i.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Naseer El Rufa'i. naij.com
Talla

Kafin yanzu dai kungiyar Malaman da hadin gwiwar kungiyar kwadago sun ci alwashin ci gaba da gudanar da yajin aikin har zuwa lokacin da bukatunsu zai biya, wajen ganin an mayar da Malaman kusan dubu 22 da Gwamnan jihar ya kora daga bakin aiki.

Gwamnatiin Jihar Kaduna Karkashin Nasir El-Rufai ta dauki matakin korar dubban malaman ne bayan da ta ce sun fadi jarrabawar gwajin da ta shirya musu.

Sai dai a lokuta da dama Kungiyoyin Kwadago na ikirarin cewa babu gaskiya a batun gwamnatin la'akari da cewa babu wani wakilci daga kungiyar kwadago ko ta malamai da gwamnatin ta kira don sanya ido kan jarabawar.

Haka Zalika Ko da gwamnatin ta yi ikirarin malaman sun gaza amsa jarabawar 'yan aji ukun Firamare, Kungiyar ta ce ba a yiwa malamai jarabawa a fannin da suka karanta ba.

Tuni dai shugabancin kungiyar malaman ta NUT reshen Kaduna, karkashin Audi Anna ya sanar da janye yajin aikin bayan kammala wani taron gaggawa, da ya kai ga bayar da dama ta biyu ga korarrun malaman su dawo bakin aiki.

A cewar wata jigo a harkar Ilmi Aishatu Gambo ta ce yajin aikin kan taka muhimmiyar rawa wajen dakushe harkokin ilmi a jihar saboda haka kamata ya yi dukkanin bangarorin biyu na gwamnati da kuma kungiyar Malaman su gyara tsakaninsu don samar da ingantaccen ilmi ga al'ummar jihar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.