Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Kotu na son majalisa ta bi matakan tsige Jacob Zuma

Ƴan adawar ƙasar ne suka garzaya kotu, inda suka zargi shugaban majalisar dokokin ƙasar da gazawa wajen binciken shugaba Jacob Zuma na ƙin bin ƙa’ida wajen yin amfani da kudin gwamnati dala miliyan 15 domin yi ma gidansa kwaskwarima.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma.
Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Kotun ƙolin ƙasar ta Afirka ta kudu ta ce majalisar dokokin ƙasar ta gaza wurin yin binciken game da zargin almundahana da dukiyar gwamnati da aka yi wa shugaba  Zuma.

Al’amarin zai iya janyo a fara bin matakan tsige shugaban ƙasar idan aka kama shi da laifi.

Al’amarin ya yi ƙamari ne a lokacin da kotun kula da kundin tsarin mulkin ƙasar ta kama shugaban da laifin karya alƙawarin da ya ɗauka, ta hanyar ƙin biyan kuɗaɗen da ya karɓa.

Kotun ta ta buƙaci majalisar da ta bi doka ba tare da ɓata lokaci ba, wajen samar da dokar da za a iya amfani da ita domin tsige shugaban ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.