Isa ga babban shafi
Afrika

"Gwamnatin Sudan ta Kudu na amfani da abinci a matsayin makami"

Tawagar masu sa’ido da majalisar dinkin duniya ta tura Sudan ta Kudu, sun shaidawa kwamitin tsaron majalisar cewa, gwamnatin Salva Kiir tana amfani da abinci a matsayin makamin yaki.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a lokacin da ya sauka a filin jiragen sama na kasar Sudan. 1 ga Nuwamba, 2017
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a lokacin da ya sauka a filin jiragen sama na kasar Sudan. 1 ga Nuwamba, 2017 REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah/File Photo
Talla

A cewar jami’an sa idon, gwamnatin Kiirr tana amfani da damarta wajen datse hanyoyin kai wa wasu yankunan kasar da ke cikin yunwa agajin abinci, lamarin da ke jefa fararen hula cikin munin yanayi.

Zalika tawagar majalisar dinkin duniyar ta ce, daga shekarar 2016 zuwa ta 2017, sojojin Sudan ta Kudu, sun kai jerin hare hare a garin Wau, da wasu yankunan da ke kewaye shi a yammacin Bahr el-Ghazal, bisa manufa ta nuna kabilanci, inda suka tilastawa sama da mutane dubu 100,000 tserewa daga gidajensu.

A cikin shekarar 2013 yakin basasa ya barke a Sudan ta Kudu, shekaru biyu bayan samun ‘yancin kai daga kasar Sudan, sakamakon takun saka da ya juye zuwa na kabilanci tsakanin Shugaban kasa Salva Kiir da mataimakinsa a waccan lokacin Riek Machar.

Rikicin yayi sanadin raba kashi daya cikin biyu na ‘yan kasar miliyan 12 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.