'Yan Togo na tserewa zuwa Ghana neman mafaka
Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira a Ghana ta ce yanzu haka daruruwan ‘yan kasar Togo ne suka tserewa zanga-zangar da ‘yan adawa ke yi domin samun mafaka a kasar.
Wallafawa ranar:
Paddy Tetteh ya ce tun ranar larabar makon jiya ‘yan gudun hijirar suka fara isa Ghanar, kuma yanzu haka adadin su ya kai 300.
Sarkin Chereponi Abdul Razak Tahiru ya ce tuni aka taimakawa bakin da abinci da tabarmi da gidajen sauro.
Tun a Makonni baya ake samun bore daga al'ummar Togo da ke nuna adawarsu da shugabancin Faure Gnassingbe wanda ke mulkin kasar tun 2005.
Mista Gnassingbe ya karbi mulkin kasar ne daga wajen mahaifinsa wanda ya shafe shekaru 38 yana jan ragamar kasar tun 1967.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu