Isa ga babban shafi
Togo

Dole Togo ta koma tsarin wa’adin shugabancin kasa sau biyu - Chambas

Jakadan majalisar dinkin duniya a yammacin nahiyar Afrika da yankin Sahel, Mohamed Ibn Chambas, ya ce tilas ne gwamnatin kasar Togo, ta mayar da wa’adin shugabancin kasar zuwa kashi biyu, domin kaucewa rikidewar zanga-zangar da ‘yan adawa ke yi, zuwa kazamin rikici.

Jakadan majalisar dinkin duniya a yammacin nahiyar Afrika da yankin Sahel, Mohamed Ibn Chambas.
Jakadan majalisar dinkin duniya a yammacin nahiyar Afrika da yankin Sahel, Mohamed Ibn Chambas. AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

Shawarar ta Ibn Chambas ta zo ne bayanda dubban ‘yan kasar suka shafe kwanaki uku suna zanga zangar neman shugaban kasa Faure Gnassingbe ya sauka, kalubale mafi karfi da iyalan gidansu suka fuskanta cikin shekaru 50 da suka shafe suna shugabancin kasar.

Ko da yake a yau Asabar, rahotanni sun tabbatar da cewa masu zanga-zangar basu fito ba, gamayyara ‘yan agawar kasar sun lashi takobin cigaba da jagorantar dubban al’ummar kasar cigaba da zanga-zangar, har sai burinsu na saukar shugaba Gnassingbe ya cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.