Isa ga babban shafi
KENYA

Odinga na shirin daukan mataki a Kenya

Jagoran ‘yan adawar Kenya Raila Odinga na nazarin matakin da zai dauka nan gaba bayan ya yi watsi da sakamakon zaben shugabancin kasar da ya ce, an tafka makudi a cikinsa.

Raila Odinga tare da magoya bayansa a babban birnin Nairobi
Raila Odinga tare da magoya bayansa a babban birnin Nairobi REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da kasashen duniya suka bukaci Odinga da ya shigar da kara a kotu don kalubalantar sakamakon a maimakon daukan wani matakin da ya saba wa ka’ida.

Raila Odinga mai shekaru 72 ya hakikance cewa, shi ne wanda ya yi nasara a zaben da ya ce an an sace kuri’ansa, yayin da ya bukaci magoya bayansa da su kaurace wa wuraren ayyukansu don nuna alhini kan mutanen da suka rasa rayukansu a hatsaniyar da ta kaure bayan zaben na makon jiya.

'Yan adawar dai sun yi zanga-zangar nuna bacin ransu game da sake zaben Uhuru Kenyatta wanda sakamakon zaben ya nuna cewa ya lashe kashi 54 na kuri’un da aka kada.

Tun bayan sanar da sakamakon ne, harkokin kasuwanci suka tsaya cak a kasar, yayin da ma’aikata suka ci gaba da zama a gida, amma dai rahotanni na baya-bayan nan na cewa, harkoki sun fara kan-kama a babban birnin Nairobi a yau Litinin saboda akasarin jama’a sun gaza jure wa zaman gida.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaba Kenyatta ya bukaci ‘yan adawar da su amince da sakamakon zaben kuma ya ce, koda ma za su yi zanga-zanga, to su gudanar da ita kamar yadda kunkdin tsarin mulki ya tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.