Isa ga babban shafi
Congo

An gano wasu manyan kaburbura a Jamhuriyyar Congo

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun sanar da samun Karin manyan kaburburar da ke dauke da gawarwaki a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo mai fama da tashin hankali, abinda ya kawo adadin irin wadannan kaburbura zuwa 80 yanzu haka.

Taswirar yankin Kasai mai fama da rikici a Jamhuriyyar Congo
Taswirar yankin Kasai mai fama da rikici a Jamhuriyyar Congo Wikimedia Commons
Talla

Mai Magana da yawun dakarun Majalisar da ke aikin samar da zaman lafiya a Congo, ya ce an gano gawarwakin ne a wurare daban-daban guda 6, lokacin da aka gudanar da bincike a Yankin Kasai mai fama da rikici.

Wasu alkalumman Cocin Katolika sun ce akalla mutane sama da 3,300 aka kashe, yayin da kusan miliyan daya da rabi suka tserewa gidajen su lokacin da mayakan Kamuina Nsapu dake bukatar ficewar sojoji daga yankin suka kaddamar da hare hare.

An samu manyan kaburburan ne a Diboko da Sumbula da ke cikin yankin Kamonia.

A bara ne rikicin ya barke a Congo bayan kabilar Kamwina Nsapu sun kalubalanci matakin shugaba Joseph Kabila na zarcewa kan madafan iko bayan cikar wa’adin mulkinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.