Gwamnati da 'Yan Tawaye a Janhuriyar Tsakiyar Afrika Sun Amince da Sulhu
Yau ne Gwamnatin kasar Janhuriyar Tsakiyar Afrika da bangaren ‘yan tawayen kasar suka sanya hannu cikin yarjejeniyar tsagaita wuta a wani taron da aka yi a Rome da niyyar kawo karshen tarzoma a fadin kasar.
Wallafawa ranar:
Ana sa ran bayan sulhun kungiyoyin dake dauke da makamai za su shiga Gwamnati domin ganin sun daina tada zaune tsaye.
Kasar Janhuriyar Tsakiyar Afrika wadda ake ganin a duniya ita ce mafi koma baya ta fannin komi, na fama da tashe-tashen hankula musamman na addini tun shekara ta 2013.
Rayukan mutane sama da 100 suka mutu yayinda wasu dubu dari suka tsere daga gidajen su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu