Isa ga babban shafi
South Sudan

Shugabannin Afrika za su magance yakin Sudan ta Kudu

Shugabannin kasashen gabashin nahiyar Afrika sun lashi takobin kawo karshen yaki da ake fafatawa a Sudan ta Kudu, yayin da suka ce, za su ga lallai an jinkirta babban zaben kasar da aka tsara gudanarwa a badi. 

Shugaba Salva Kiir da Riek Machar
Shugaba Salva Kiir da Riek Machar REUTERS/Stringer
Talla

Shugabannin kasashen sun bayyana bayan wani taro da suka yi a Habasha cewa, za su samar da tsari ta yadda bangarorin da ba sa ga maciji za su zauna da juna domin sulhu a karkashin yarjejeniyar da ka yi watsi da ita shekaru 3 da suka gabata, abin da ya kai ga fadan kabilanci har ya  zama mummunan yaki.
 

A cewar shugabannin, za su hanzarta fitar da tsarin zaman sulhun nan bada dadewa ba.

Yaki ya kaure ne tun shekara ta 2013 bayan Shugan Sudan ta Kudun Salva Kirr ya kori mataimakinsa Riek Machar, shekaru biyu kachal bayan sun sami ‘yancin kai daga kasar Sudan.

A mafi tarin lokaci, tattaunawar sulhun Sudan ta Kudu na sukurkucewa, domin ko a cikin shekara ta 2015, shugaba Salva Kiir da Reik Machar sun sanya hannu cikin wata yarjejeniya amma kuma ba a kai ko ina ba zancen ya shiririce..

Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu mai ci yanzu ya nemi a hana tsohon mataimakin shugaban, Reik Machar halartar duk wani taron sulhu.
 

A nata bangare dai Majalisr Dinkin Duniya ta bayyana yakin Sudan ta Kudu a matsayin yunkurin shafe wata al'umma daga daga doron kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.