Isa ga babban shafi
Najeriya

Rashin tallafin kudi na barazana ga aikin ciyar da ‘yan gudun hijirar Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Matsalar karancin tallafin kudi zai tursasawa kungiyoyin agaji dakatar da aikin ciyar da ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Sansanin 'Yan gudun hijira a Gamboru Ngala a Borno
Sansanin 'Yan gudun hijira a Gamboru Ngala a Borno REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsalar rashin kudin zai shafi ci gaban da aka samu wajen hidima da ‘yan gudun hijirar na Boko Haram.

Tun da farko hukumar samar da abinci ta duniya WFP ta bayyana cewa kusan mutane miliyan biyu ke fuskantar barazanar yunwa a arewa maso gabashi.

Rahoton hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 5 ke matukar bukatar agajin abinci a jihohi uku da suka yi fama da rikicin Boko Haram.

OCHA ta ce karancin kudin zai tursasawa wasu kungiyoyin agaji rage adadin agajin abincin da suke rarrabawa ‘yan gudun hijira.

Matsalar tsaro da ake ci gaba da fuskanta ya takaita zirga-zirga da hada-hadar kasuwanci tare da dakatar da ayyukan noma a yankin da ke dogaro da arzikin noma da kamun kifi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar kudi sama da dala biliyan 1 a bana domin ayyukan jin-kai a yankin da suka hada da samar da abinci da magani da ruwan sha da kuma bukatu na kula da ilimin ‘yan gudun hijira da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.