Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a yi bincike akan zargin lalata da ‘Yan gudun hijira

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin gudanar da bincike kan zargin Jami’an tsaro na lalata da mata da yara a sansanin ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram haram ya raba da gidajensu a Jihar Borno.

Mata da yara sun taru a wani sansanin yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Abuja
Mata da yara sun taru a wani sansanin yan gudun hijirar rikicin Boko Haram a Abuja REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Rahoton da Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta fitar ya zargi ‘Yan Sanda da sojojin kasar da yin lalata da Mata a sansanonin ‘Yan gudun hijirar Boko Haram a Maiduguri.

Kungiyar ta ce tana da rahotanni 43 daga mata da ‘yan matan da aka yi lalata da su da wadanda aka yi wa fyade.

Malam Garba Shehu, da ke Magana da yawun Buhari, ya ce shugaban na sane da abin da ke kunshe a cikin rahoton Human Rights Watch kuma ya ba hukumar ‘Yan sanda umurnin gudanar da bincike a sansanonin ‘Yan gudun hijirar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.