Isa ga babban shafi
OPEC

Equatorial Guinea ta zama mamba a OPEC

Equatorial Guinea ta kasance kasa ta 6 daga Nahiyar Afirka da ta zama mamba a kungiyar kasashen duniya masu arzikin man fetur wato OPEC, kamar yadda wasu majiyoyi a taron kungiyar da ake gudanarwa a Vienna ta tabbatar.

Taron kasashen OPEC a Vienna
Taron kasashen OPEC a Vienna REUTERS
Talla

Ministan albarkatun mai na kasar Saudiyya Khaled Al-Faleh wanda ke halartar taron kasashen masu arzikin mai a birnin Vienna na kasar Austria, ne ya sanar da cewa an amince da bukatar Equatorial Guinea domin kasancewa mamba a kungiyar, inda a yanzu adadinsu ya tashi kasashe 14.

A cikin watan Janairun da ya gabata ne ministan ma’adinai da kuma albarkatun man fetur na kasar Gabriel Bbaga Obiang Lima ya gabatar da bukatar kasancewa mamba a kungiyar, bukatar da aka amince da ita a yau alhamis.

Matakin dai zai taimakawa tattalin arzikin Equatorial Guinea da karawa Afrika karfin fada aji a kungiyar OPEC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.