Kano
An yi Jana’izar uwar gidan Malam Aminu Kano
An gudanar da Jana'izar uwar Gidan Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a yau Litinin wadda ta rasu bayan fama da doguwar jinya a birnin Kano. Marigayiya Shatu Aminu Kano ta rasu tana da shekaru 89 a duniya.
Wallafawa ranar:
Talla
Marigayiyar Shatu Aminu Kano ta rasu ta bar jikoki 15.
Ta rasu bayan shekaru 34 da rasuwar mijinta Malam Aminu Kano fitaccen dan siyasa a arewacin Najeriya wanda ya kafa jam’iyyar NEPU ta masu ra’ayin rikau.
Tsohon shugabannin hukumar Zaben Najeriya INEC Farfesa Attahiru Jega ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kamar maza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu