Najeriya
Kungiyar Boko Haram ta sako wasu daga cikin yan matan Chibok
Rahotanni Daga Najeriya sun ce kungiyar Boko Haram ta saki Yan Matan Chibok da dama da ta sace sama da shekaru biyu sakamakon tattaunawar da suka yi da gwamnati.
Wallafawa ranar:
Talla
Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance dake tabbatar da adadin Yan Matan da aka sake, amma kafofin yada labarai da dama sun jiyo daga jami’an tsaro cewar adadin ya kai 80, kuma yanzu haka Yan Matan na Banki dake kusa da iyakar Kamaru.
Ana saran Gwamnatin Najeriya tayi Karin haske akai nan gaba kadan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu