Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia za ta kafa hukumar binciken Jammeh

Gwamnatin Gambia za ta kafa hukumar tabbatar da gaskiya da sasanta rikici wadda za ta gudanar da bincike kan barnar da aka tafka a zamanin gwamnatin Yahya Jammeh.

Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh a lokacin da ya ke ficewa daga kasar bayan mika mulki ga Adama Barrow
Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh a lokacin da ya ke ficewa daga kasar bayan mika mulki ga Adama Barrow ©Thierry Gouegnon/REUTERS
Talla

Ministan Shari’a na kasar Abubacarr Tambadou ya ce, hukumar za ta binciki dukiyar tsohon shugaban da ya sha kaye a hannun Adama Barrow.

Kazalika za a karfafa wa jama’a gwiwa don bada shedar miyagun ayyauakn da aka aikata a lokacin Jammeh, sannan kuma za a biya diyya ga wadanda aka ci zarafinsu.

Ana zargin tsohuwar gwamnatin da ta shafe shakaru 22 kan karaga da azabtar da jama’a, abin da ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Kazalika ana zargin cewa, fiye da Dala miliyan 11 ya yi batan dabo daga asusun gwamnati bayan Jammeh ya fice daga kasar a cikin watan Janairun da ya gabata, wato bayan ya shafa matsin lambar mika mulki daga shugabannin Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.