Isa ga babban shafi
Najeriya

Shekau ya yi barazanar ci gaba da kai hari a Maiduguri

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya sake fitowa a wani hoton bidiyo inda ya ke ikirarin daukar alhakin hare haren kunar bakin wake da aka kai a garin Maiduguri Jihar Borno.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau AFP PHOTO / YOUTUBE
Talla

A cikin sakon bidiyon, shekau ya ce sun gwabza fada da sojoji a kan iyakar kamaru tare da karyata ikirarin gwamnatin kasar da ta ce ta kashe mayakan shi 60 cafke wasu 20 da kuma kubutar da mutane sama da 5,000 a makwannin da suka gabata.

A hoton bidiyon na tsawon minti 27 , shugaban na Boko Haram ya ce yana nan garau tare da karyata ikirarin an raunana shi.

Sai dai kuma yanayinsa da babatunsa ba kamar yadda ya saba ba, a hoton bidiyon da ya fito tare mayakansa biyu a bayansa sun rufe fuska rike da makami.

Wannan ne karon farko da shekau ya fito tun fitowarsa a hoton bidiyo a watan Disemban bara lokacin da sojojin Najeriya suka ce sun kakkabe ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.