Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta umarci taimakawa kungiyoyin agaji na duniya don tallafawa Sudan ta Kudu

Shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan ya umarci jami'an Gwamnati da su taimakawa kungiyoyin ayyukan jinkai na duniya wajen kai kayan agaji ga dimbin mabukata dake kasar Sudan ta Kudu.

Shugaban Sudan Omar al-Bashir tare da takwaransa na Sudan ta Kudu  President Salva Kiir
Shugaban Sudan Omar al-Bashir tare da takwaransa na Sudan ta Kudu President Salva Kiir Reuters/Adriane Ohanesian
Talla

Tun ranar Juma'a da ta gabata ne dai aka sanar da cewa Sudan ta Kudu na fuskantar yunwa, inda mutane dubu dari ke cikin halin wahala, wasu mutanen miliyan daya kuma na gab da shiga wani hali.

Ministan waje na Sudan Ibrahim Ghandour ya fadi cewa Shugaba Omar al-Bashir ya bada umarnin a bi ta kasar da kayayyakin taimako domin kai kayan agaji zuwa Sudan ta Kudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.