Sudan ta Kudu
Rikici ya sake barkewa a Sudan ta Kudu
Rahotanni daga Sudan ta Kudu sun ce, an samu barkewar tashin hankali a Malakal, birni na biyu mafi girma a kasar kuma cibiyar hakar man fetur.
Wallafawa ranar:
Talla
Kakakin sojin Sudan ta Kudu, Kanar Santo Domic Chol ya ce, 'yan tawayen sun dade suna neman tada hankali bayan zaman lafiyar da aka samu a yankin.
Sai dai kakakin 'yan tawayen Gatjiath Deng, ya zargi sojojin ne da kaddamar da hari a sansaninsu.
Deng ya ce, dakarun sun yi nasarar kassara sojojin gwamnati a karawar da aka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu