Isa ga babban shafi
Nijar

An dage shari’ar Hama Amadou kan safarar yara a Nijar

Kotun Nijar a Yamai ta dage shari’ar zargin safarar kananan yara da ta shafi madugun adawar kasar Hama Amadou har zuwa ranar 13 ga watan Maris, kamar yadda lauyoyin da ke kare tsohon Firaministan suka bukata.

Hama Amadou, tsohon Firaministan Nijar kuma madugun adawa
Hama Amadou, tsohon Firaministan Nijar kuma madugun adawa ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Ali Kadri daya daga cikin Lauyoyin da ke kare Hama, ya ce kotun ta amince da bukatarsu kuma ta dage sauraren Shari’ar zuwa 13 ga Maris.

Ya ce sun bukaci dage shari’ar ne domin bayar da dama ga tsohon Firaministan ya dawo tare da yin kiran janye siyasa a shari’ar.

Sannan lauyoyin sun bukaci cikakken bayani na tuhume tuhumen da ake wa Hama daga babban mai shigar da kara na Nijar.

Ana tuhumar Hama Amadou da wasu mutane 20 da suka hada da manyan ‘Yan siyasar Nijar da laifin safarar yara daga Najeriya.

Batun dai ya haifar da rudani a siyasar Nijar.

A ranar 16 ga watan Maris na bara ne aka garzaya da Hama zuwa Asibitin Faransa daga gidan kaso a yayin da ya rage kwanaki a gudanar da zabe zagaye na biyu tsakanin shi da Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou.

‘Yan adawa sun kauracewa zaben saboda rashin sakin Hama, tare da yin watsi da sakamakon zaben da Issoufou ya lashe da sama da kashi 92.

Hama Amadou babban mai adawa da shugaba Issoufou ya fice Nijar ne a watan Agustan 2015 bayan majalisa ta amince a kaddamar da bincike akansa game da badakalar mallakar ‘ya'ya ba bisa ka’ida ba da aka yi wa Matarsa fataucinsu daga Najeriya zuwa Cotonou.

Hama Amadou ya ce zargin yarfe ne na siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.