Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sandan Najeriya sun kwato kudi daga Jami’an hukumar Zabe

Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta yi nasarar kwato naira miliyan 111 daga hannun wasu jami’an hukumar zaben kasar da suka yi aiki a Jihar Rivers lokacin da aka yi zaben cike gurbin ‘Yan Majalisun Tarayya.

Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu inec
Talla

Jami’an hukumar zaben mai zaman kanta INEC 23 ne ake tuhuma sun karbi makudan kudaden daga hannun gwamnatin Rivers.

Shugaban kwamitin binciken da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan kasar Ibrahim Idris ya kafa, DCP Damian Okoro ya bayyana cewar manyan jami’an Hukumar zaben uku sun karbi miliyan 20 kowannesu daga cikin cikin miliyan 360 da Gwamna Nyeson Wike ya ba su, yayin da sauran kuma kowa ya karbi miliyan 15.

Gwamna Wike dai ya yi watsi da zargin, yayin da rundunar ‘Yan Sandan ta kori jami’anta da ake zargi da hannu wajen karbar cin hanci, tare da yin alkawalin gurfanar da duk wanda ke da hannu wajen cin hanci a gaban shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.