An kama Tsohon Ministan Gambia a Switzerland
Jami’an Tsaro a kasar Switzerland sun kama tsohon ministan harkokin cikin gidan Gambia Ousman Sonko wanda ake zargi da laifufukan cin zarafin Bil Adama lokacin mulkin Yahya Jammeh.
Wallafawa ranar:
Mai gabatar da kara Cristof Scheurer ya ce ana binciken tsohon ministan a karkashin dokar kasar mai lamba 264.
Sonko ya dade yana shugabancin jami’an tsaron fadar shugaban kasa kafin a nada shi ministan cikin gida.
Yanzu haka tsohon jami’in na a tsare a hannun jami’an tsaro a birnin Bern na Switzerland.
A watan Satumba ne Jammeh ya tube Sonko daga mukamin minister kuma lokacin ne ya tsere zuwa Turai inda Sweden ta ki ba shi mafaka.
Rahotanni sun ce a watan Nuwamba ya nemi mafaka a Switzerland.
Wannan na zuwa a yayin da sabon shugaban Gambia Adama Barrow ya koma Banjul daga Senegal bayan ficewar Jammeh da ya mulki Gambia a tsawon shekaru 22.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu