Bisa dukkan alamu dai Gwamnatin sabon Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ta kama aiki sosai domin ganin kasar ta shiga gudanar da ayyukan da aka zabe ta ta yi, Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero a jihar Kanon Najeriya ya yi sharhi kan kalubalen dake gaban sabon shugaban.
Sauran kashi-kashi
-
Farfesa Kailani Muhammed a kan batun satar danyen mai a Najeriya
Hukumomin Najeriya sun ce sun kama jiragen ruwa 14 da ake satar danyan man fetur a Neja Delta tsakanin watan Janairun wannan shekara zuwa karshen watan Maris.Rundunar dake aikin samar da tsaro a Jihar Rivers tace wannan bai hada da kananan jirage 90 da kuma mutane 74 da ta kama ba, wadanda ke yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Kelaini Muhammed, masani a kan harkar gas da man fetur, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.14/05/202403:31 -
Kwamandan MNJTF Janar Ibrahim Sallau kan nasarar su a yankin tafkin Chadi
Rundunar hadin gwuiwa da ke yaƙi da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi da ake kira MNJTF ta sanar da kashe mayaka 299 a cikin watanni 10 da suka gabata da kuma samun wasu 273 da suka mika kansu cikin lumana. Kwamandan rundunar Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali ya bayyana haka ga Babban Editan sashin Hausa Bashir Ibrahim Idris a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho bayan ya kwashe watanni 10 yana jagorancin rundunar mai cibiya a kasar Chadi.Ku latsa alamar sauti domin sauraren zantawar su.09/05/202406:33 -
Farfesa Dicko Abdurrahmae kan zaben Chadi
Yau Litinin aka bude rumfunan zabe a kasar Chadi, don zaben shugaban kasa da zai kafa sabuwar gwamnatin Chadi da ta kasance karkashin mulkin soji na tsahon shekaru 3.06/05/202403:30 -
Farfesa Umar Pate: Kan Ranar 'Yancin 'Yan Jarida ta Duniya
Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma’aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin.03/05/202403:41 -
Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya
Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.02/05/202403:06