Isa ga babban shafi
Mali

Tarayyar Turai ta tsawaita ayyukan sojinta a Mali

Kungiyar Tarayyar Turai ta tsawaita wa’adin ayyukan jami’anta a kasar Mali har shekaru biyu masu zuwa. Kuma Babbar manufar tsawaita wa’adin aikin rundunar ita ce ci gaba da bayar da horo ga jami’an tsaron kasar ta Mali da yanzu haka ke fama da matsalar tsaro.

Rundunar Sojin Barkhane ta Faransa da ke aikin wanzar da tsaro a Mali
Rundunar Sojin Barkhane ta Faransa da ke aikin wanzar da tsaro a Mali RFI/ Anthony Fouchard
Talla

Sanarwar da Hukumar kungiyar ta Turai ta fitar ta ce Dakarunta za su ci gaba da aiki a Mali har zuwa ranar 14 ga watan Janairun shekara ta 2019, kuma babban aikinsu shi ne ci gaba da bai wa jami’an tsaron kasar horo.

Tun shekara ta 2014 ne dai kasashen na Turai suka fara aikin taimaka wa sojoji da ‘yan sanda da kuma jandarma na kasar ta Mali, domin tabbatar da tsaro bayan kwato yankunan kasar daga hannun ‘yan ta’adda.

Kungiyar Turai ta ware kudaden da yawansu ya kai kusan yuro milyan 30 domin tafiyar da wannan aiki a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Ko baya ga jami’an na kasashen Turai da ke bayar da horo, akwai kuma wata runduna ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kunshe da dakaru dubu 11 da ke aikin wanzar da tsaro da zaman lafiya a wannan kasa mai fadin murabba’in kilomita milyan daya da dubu 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.