Isa ga babban shafi
Nijar

An cafke Jami’an da ke tsarawa dalibai takardun Jabu a Maradi

Jami’an ma’aikatar ilimi su uku ne aka cafke yayin da ake neman na hudu bisa zargin karbar na goro domin sake da dawo da daliban sakandare sama da 300 da aka kora daga makarantun gwamnati ta barauniyar hanya a jihar Maradi da ke jamhuriyar Nijar.

Harabar shiga kofar Jami'ar Fasaha a Maradi Jamhuriyyar Nijar
Harabar shiga kofar Jami'ar Fasaha a Maradi Jamhuriyyar Nijar RFI/Salisu Issa
Talla

Wasu daga cikin daliban kuwa an ba su damar ci gaba da karatun ne ta hanyar tsara ma su takardun jabu.

Daraktan sashen ilimin sakadare da ke kula da jihar ta Maradi Illo Bija ya ce kame Jami’an ya zama wajibi domin tabbatar da muhimmacin Ilimi a Nijar.

Illo Bija ya ce takardun Jabu da aka samu a Maradi sun kai 140 kuma an yi nasarar kame babban jami’in da ke aikin bayar da takardun.

Sannan hukumomin Ilimin sun ja kunnen Dalibai su guji yin amfani da takardun Jabu domin duk wanda aka kama za a hukunta shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.