Isa ga babban shafi
Najeriya

Muna nan da karfinmu, za mu ci gaba da yaki- Shekau

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a wani faifan bidiyo inda ya ke musanta ikirarin gwamnatin Najeriya na fatattakarsu tare da murkushe su a Dajin Sambisa, sansanin da suke garkuwa da mutane da jagorantar hare hare.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a tsakiyar mayakansa
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a tsakiyar mayakansa HO / BOKO HARAM AFP / AFP
Talla

“Muna nan lafiya, kuma ba wanda ya kore mu zuwa ko ina” in ji Shakau a cikin sakon bidiyon na tsawon mintina 25 da ya fitar yana magana a harshen Larabci da Hausa.

Shekau ya ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na yi wa mutane karya, wanda a jajibirin Kirsimeti ya bayyana cewa an murkushe ‘Yan Boko Haram tare da korarsu a Dajin Sambisa.

Shugaban na Boko Haram ya fadi a cikin sakon bidiyon cewa babu wata dabara da za ta iya fallasa inda suke buya sai idan Allah ya yarda.

Shekau dai ya sha fitowa yana karyata ikirarin Sojoji akan samun nasarar Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.