Isa ga babban shafi
Sudan

Gwamnatin Sudan ta yi barazanar murkushe 'yan adawa

Shugaban Sudan Umar Hassan Al-Bashir ya yi barazanar yin amfani da karfi domin murkushe masu adawa da shi.

Shugaban kasar Sudan Oumar al-Bashir
Shugaban kasar Sudan Oumar al-Bashir REUTERS
Talla

Alwashin shugaban na Sudan na zuwa a daidai lokacin da ‘yan adawa a kasar suka yi kira da a gudanar da yajin aiki na tsawon kwanaki biyu a cikin makon gobe.

‘Yan adawar sun ce tilas su yi wannan gangami domin hawa kujerar naki kan matakin da gwamnatin kasar zata dauka na rage yawan tallafin da take bayarwa da ke saukaka farashinsa, matakin da ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kasar harma da magunguna.

A shekara ta 2013, jami’an tsaron Suda sun yi amfani da karfi kan wasu masu zanga zangar hamayya da gwamnatin al-Bashir, da ya kai ga sun kashe mutane da dama lokacin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.