Isa ga babban shafi
Canjin Yanayi

Yarjejeniyar canjin yanayi na birnin Paris zai soma aiki

A yau Juma’a ne yarjejeniyar canjin yanayi da aka amince a birnin Paris za ta soma aiki, yayin da ya rage kwanaki uku a bude wani babban taron MDD a Morocco domin tattauna yadda za a aiwatar da yarjeniyar da kasashe 196 suka amince da ta shafi rage dumamar yanayi a duniya 

Canjin yanayi a Duniya
Canjin yanayi a Duniya
Talla

Yarjejeniyar canjin yanayin da aka kai ruwa-rana kafin kasashe 196 su amince a birnin Paris a yau Juma’a zata soma aiki yayin da ake shirin bude wani babban taro a Morocco inda za a yi matsin lamba wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar.

Muhimmin batu a yarjjeniyar shi ne yadda za a rage dumamar yanayi daga gurbataccen iskan daga kasashe masu manyan masana’antu

Sai dai kuma wani rahoton da hukumar kare muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce ko da ace an cimma alkawurran da aka dauka a yarjejeniyar Paris amma zafin da ke dumama duniya zai kai kashi uku na ma’ainin Celsius a karshen karni

Kuma wani muhimmin batu a yarjejeniyar da ake samun sabani shi ne game da kudaden diyya da manyan kasashe masu masana’antu zasu dinga ba kananan kasashe da dumamamr yanayin ke wa illa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.