Shan giya na kara cutar sankarar mama ga mata.
Wani binciken masana kiwon lafiya ya nuna cewar mutane sama da 700,000 suka kamu da cutar sankara sakamakon kwankwadar barasa ko kuma giya, kuma tuni 366,000 sun sheka lahira a shekarar 2012.
Wallafawa ranar:
Kevin Shield, daya daga cikin masanan da suka gudanar da bincike yace akasarin masu kwankwadar barasan basu ma san tana haifar da cutar sankarar ba.
Masanan sun ce giya na haifar da kashi biyar na sabbin masu kamuwa da cutar sankara a duniya, kuma kashi 4.5 na mutuwa kowacce shekara.
Rahotan da aka gabatar wajen taron masana cutar kansa ta duniya a Paris yace lallai giya na zafafa cutar sankarar mama a mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu