Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

An kori kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya bisa laifin yin sakaci

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya kori kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu bayan wani rahoton da ya nuna gazawar rundunar wajen kare lafiyar fararen hula a rikicin da ya barke a birnin Juba.

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Juba.
Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Juba. UN Photo/Eric Kanalstein
Talla

Mr Ban ya bukaci sauya kwamandan da wani jami’in nan take kamar yadda mai magana da yawun Majalisar, Stephane Dujarric ya sanar.

Binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ya nuna cewa, rashin kyakyawan jagoranci a rundunar wanzar da zaman lafiyar ne ya haifar da rauni wajen kai wa fararen hulan doki a rikicin da aka yi a baya-bayan nan tsakanin ranakun 8-11 ga watan Yuli a birnin na Juba.

Binciken dai ya gano cewa, dakarun sun ki sadaukar da ransu wajen bai wa fararen hular kariya.

A bangare guda kuma, binciken bai tabbatar da zarge-zagen da ake yi wa dakarun ba dangane da rashin tabuka komai ba a lokacin da aka yi lalata da mata a gaban idanunsu a ranakun 17 zuwa 18 na Yuli.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.