Isa ga babban shafi
Somalia

Mutane 75,000 sun tsere daga gidajensu

Majalisar Dinkin Duniya tace mutane 75,000 ne suka tsere gidajen su a kasar Somalia, yayin da 18 suka mutu sakamakon tashin hankalin da aka kwashe makwanni uku anayi a kasar.

'Yan gudun hijra daga Somalia, da ke sansanin Daadab a arewacin Kenya
'Yan gudun hijra daga Somalia, da ke sansanin Daadab a arewacin Kenya UNHCR - kenya
Talla

Ofishin jinkai na Majalisar yace fargabar cewa tashin hankalin na iya daukar dogon lokaci ne ya tilastawa dubban mutane tserewa gidajen su.

Ofishin ya kuma bayyana fargabar cewar ganin yadda ake tsakiyar damuna mutanen zasu fuskanci matukar wahala musamman mata da kanana yara.

Mafi yawa daga cikin ‘yan gudun hijarar Mata ne sai kuma kananan yara da tsofaffi.

Tun ranar Asabar ne fadan ya barke tsakanin jama’ar yankunan Puntland da Galmudug a garin Galkayo.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.