An kai harin Bam yayin taro kan tsaro a Mogadishu
Kungiyar Al-shabab ta kai hari a wani otel da ke kusa da fadar shugaban kasar a birnin Mogadishu, Harin daya halaka mutane 22 a wannan talata.
Wallafawa ranar:
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba, da ‘yan kungiyar ta Alshabab ke kai hari a wannan otel da ake sauke manyan baki da kuma sauran jami’an gwamanati a cikinsa ba.
Rahotanni sun ce ana gudanar da wani taro kan yadda za’a shawo kan matsalolin tsaron kasar, a dai dai lokacin da aka kai harin.
Kimanin shekaru biyar da suka gabata, dakarun Tarayyar Afrika AU suka samu nasarar korar mayakan al-Shabbab daga babban birnin Somalia Mogadishu, sai dai har yanzu mayakan suna cigaba da kai hare-haren kunar bakin wake, da kuma tada bama bamai a sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu