Isa ga babban shafi
Somalia

Kisan Jagoran Shaabab A Somalia Ya Haifar da Mummunan Hari a Wani Otel Dake Mogadishu

An kai wani kazamin hari cikin wani Otel dake karban bakuncin manyan mutane a birnin Mogadishu na Somalia jim kadan bayan da kasar Amurka ta sanar da kashe jagoran Kungiyar Shaabab a  Somalia Abdullahi Haji Da’ud a wani hari ta sama da Soja suka kai.  

Mayakan kungiyar Al-Shaabab
Mayakan kungiyar Al-Shaabab rfi
Talla

Peter Cook mai Magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya bayar.

Yau Laraba an sami kai munanan hare-hare a wani kasaitaccen Otel mai suna Ambassador Otel dake birnin Mogadishu inda manyan jami'ai na kasar da kuma baki ke zama.

Majiyoyi na cewa mutane da yawa ake ganin sun rasa rayukansu sakamakon wannan hari.

‘Yan kungiyar Shaabab da Kungiyar Al-Qaeda tun shekara ta 2011 aka kore su, amma kuma yanzu haka sun zame wa Somalia da makwabciyar ta Kenya abin tsoro saboda kai hare-hare da suke yi kasashen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.