Isa ga babban shafi
Afrika

Jam'iyyar ANC na fuskantar kalubale a zabuka

Yayin da ake cigaba da karbar sakamakon kada kuri’a a kasar Afirka ta Kudu, rahotanni na nuni da cewa jam’iyya mai mulki a kasar, wato ANC na fuskantar kalubale mafi girma daga yan adawar kasar a zaben kananan hukumomin da ya gudana.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma yayin taron Jam'iyyar ANC
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma yayin taron Jam'iyyar ANC REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Kawo yanzu an karbi kimanin kashi 80% daga cikin kuri’un da aka kada.

Jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance ce ke jagaba a biranen Port Elizabeth da kuma Cape Town, wadanda suke da muhimmanci a kasar yayinda a Johannesburg da Pretoria kuma jam’iyyar mai mulki ta ANC da Demokratic Alliance ke kan-kan-kan.

Ana ganin zargin aikata cin hanci da rashawa da ake yiwa shugaban Afirka ta Kudun Jacob Zuma da kuma matsalar rashin aikin yi da take ciwa mutanen kasar tuwo a kwarya ne ke tasiri wajen koma bayan da Jam’iyya mai mulki ke samu.

Wanna dai shine karo na farko da Jam’iyyar ANC da gamu da adawa mai zafi daga bangaren yan adawar kasar tun bayan fara mulkin dimokaradiyya a Afirka ta Kudun 1994 inda ta saba lashe kashi 60% na zaben kananan hukumomin.

Kawo yanzu alkalumma sun nuna cewa ANC na jagaba da kashi 52%, democratic alliance kasha 30% sai kuma jam’iyyar EFF mai biye musu da kashi 7%.

Zaban kananan hukumomin na zama zakaran gwajin dafi ga babban zaben kasar da zai gudana a 2019
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.