Jam’iyyar ANC mai mulkin Afrika ta Kudu ta koyi darasi
Jam’iyyar ANC mai mulkin Afrika ta Kudu ta ce, ta koyi darasi a zaben kananan hukumomi da aka gudanar, inda sakamakon zaben ke nuna cewa, al’ummar kasar sun dawo daga rakiyar jam’iyyar.
Wallafawa ranar:
Jam’iyyar ANC wadda ta fara mulkin kasar tun shekara ta 1994, bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata ta fuskanci babban koma baya a wannan karon, batun dake nuna farin jinin ta na gab da disashewa.
Duk da dai jumullar sakamako na nuna cewa, jam’iyyar na kan gaba, ta samu koma bayan da bata taba ganin irinsa ba cikin shekaru 22.
Al'ummar Afrika ta Kudu na cigaba da bayyana takaicinsu dangane da durkushewar tattalin arziki da rashin ayyukan dake cigaba da yi musu katutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu