Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta kammala aikin soji a CAR

Shugaban Faransa Francois Hollande ya sanar cewa a cikin watan Oktoba mai zuwa ne kasar za ta kawo karshen tura soji maido da zaman lafiya a Jamhuriyar tsakiyar Afrika. 

Faransa za ta kawo karshen tura sohinta zuwa Afrika ta Tsakiya
Faransa za ta kawo karshen tura sohinta zuwa Afrika ta Tsakiya AFP PHOTO / ERIC FEFERBERG
Talla

Shugaba Hollande wanda ya ke jawabi a wani taro da jami'an ma'aikatar tsaron kasar a birnin Paris ya fadi ce, ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian zai nufi Jamhuriyar Tsakiyar Africa a cikin watan Oktober, domin bayyana kawo karshen girke sojan Faransa a Bangui da ake kira Operation Sangari.

Tun a watan 12 na shekara ta 2013 Faransa ta kaddamar da Operation Sangari da niyyar kawo karshen kazamin fada tsakanin musulmai da kiristioci da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, yayin da fiye da rabin miliyan suka tsere daga muhallinsu.

Dakarun Faransa dubu 2 da 500 ke cikin shirin, amma a watan Yuni aka rage yawansu zuwa 350.

Ita ma dai Majalisar dinkin duniya ta tura karin dakarun wanzar da zaman lafiya da suka hada da soja da ‘yan sanda dubu 12 da 600 da karin fararen hula 500 duk dai domin tabbatar da zaman lafiya a kasar Afrika ta Tsakiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.